RANA IRIN TA YAU A TARIHI 2/1/2023
2 ga Janairu, shekarar 1492
![]() |
| Spain ta sake karɓo Granada |
A wannan rana a shekarar 1492, Granada, gidan sarautar Alhambra, fada da kuma babban birni na ƙarshe na masarautar Moorish a Spaniya, ya miƙa wuya ga Sarakunan Katolika, Ferdinand II da Isabella I, wanda ya kawo ƙarshen mamayewar da ake musu.
Ƙarin haske: Moorish daga Moors sune musulman da suka mulki Spaniya, Andalus a wancan lokacin.
2 ga Janairu, shekarar 1905
![]() |
Rundunar ƴan sandan Rasha ta mika wuya a tashar jiragen ruwa ta Port Arthur |
A lokacin yaƙin Russo-Japan ƴaki tsakanin Rasha da Japan, Port Arthur, sansanin sojojin ruwa na Rasha a ƙasar Sin, ya faɗa hannun sojojin ruwan Japan karkashin Admiral Heihachiro Togo.
2 ga Janairu, shekarar 1863
![]() |
Yaƙin Stones River |
Yaƙin Stones River ya zo ƙarshe a lokacin yaƙin basasar Amurka; ko da yake ba a ayyana hakan ba, arangamar wata ce nasara ce ga sojojin ƙungiyar, waɗanda Janar William S. Rosecrans ya jagoranta.
Ƙarin haske: Stones River wani rafi ne da yake ƙasar Amurka.
2 ga Janairu, shekarar 1896
![]() |
| An haifi Dziga Vertov |
Dziga Vertov, darektan hoto mai motsi na Soviet wanda ƙa'idar sa da ya fitar ta kino-glaz ta yi tasiri a duniya kan ci gaban harkokin shirin fim da sinima cikin shekara 1920s, aka haife shi.
2 Jan, shekarar 2004
![]() |
| Aiken Stardust |
Jirgin sama jannati na NASA Stardust ya tattara garin ƙura daga tauraruwa mai wutsiya 2, wanda daga baya aka gano yana ɗauke da amino acid glycine, muhimmin tubalin gina rayuwa.
Ƙarin haske: NASA tashar binciken kimiyya ta sararin samaniya ta Ƙasar Amurka
Amino Acid Glycine wani sinadari ne da jikin murum ke ɗauke da shi





Comments
Post a Comment