Menene amfanin sanin tarihi? (2)
Yana koyar da bayyanannen darasi
1. Sanin Siyasa
Tarihi zai iya taimaka mana mu zama nagartattun ƴan ƙasa masu ilimi. Ya nuna mana ko su wanene mu a matsayinmu na gamayya, kuma sanin wannan muhimmin abu ne na tabbatar da al'ummar dimokuradiyya. Wannan ilimin yana taimaka wa mutane su taka rawar gani a fagen siyasa ta hanyar muhawara ta ilimi da kuma fayyace ainihin imanin mutane. Ta hanyar ilimin tarihi, 'yan ƙasa za su iya canza tsoffin tsarukan da aka yadda dasu a baya.
2. Tarihi Yana Koyar Da Ɗa'a Da Ɗabi'u
Ta hanyar kallon kebantaccen labarai na daidaikun mutane da yanayi, zaku iya gwada ɗabi'u da ƙimar ku. Kuna iya kwatanta shi da wasu yanayi na wahala da mutane suka fuskanta a lokutan wahala. Kallon mutanen da suka fuskanci kuma suka shawo kan wahala na iya zama da ban sha'awa. Kuna iya yin nazarin manyan mutanen tarihi waɗanda suka yi nasara ta hanyar matsalolin ɗabi'a, da kuma talakawa waɗanda ke koya mana darussa cikin ƙarfin hali, dagiya da kuma yin zanga-zanga.
3. Yana Gina Ingantaccen Ɗan Kasa
Sanin tarihi wani al'amari ne da ba sai an yi muhawara kan sanyawa zama ingantaccen ɗan ƙasa ba. Wannan yana daya daga cikin manyan dalilan da ya sa ake koyar da shi a matsayin darasi a makaranta. Mutanen da ke karanta ko koyar da tarihin zama ɗan ƙasa suna son su inganta nagartaccen asalin ƙasa har ma da amincin ƙasa ta hanyar koyar da darussan nasarar dai-daikun mutane dama kungiyoyi.
4. Koyi Daga Abubuwan Da suka Gabata Kuma Ku Sukai Nni da Bayyanannun Alamomin Gargaɗ i
Muna koyi daga zaluncin da aka yi wa gungun mutane a baya; kisan ƙare dangi, yaƙe-yaƙe, da hare-hare. Ta wannan wahala ta zalunci mun koyi kula da alamun gargaɗin da ke haifar da irin wannan zalunci. Al'umma sun sami damar ɗaukar waɗannan alamun gargaɗin da kuma kau da su idan sun gan su a yau. Sanin abubuwan da suka faru suka haifar da waɗannan yaƙe-yaƙe daban-daban yana taimaka mana sosai kuma zai yi tasiri a rayuwar mu nan gaba.
5. Samun Abin Dogaro Da Kai
Amfanin sani da kuma Ƙwarewa game da tarihi ke bada damar yin tunani mai mahimmanci, bincike, tantance bayanai, da dai sauransu, duk waɗannan ƙwarewa ne masu muhimmanci waɗanda masu aiki ke nema. Yawancin ma'aikata suna ganin waɗannan ƙwarewa a matsayin wata kadara a cikin ma'aikatansu kuma za su ɗauki waɗanda ke da suka san tarihi a cikin ayyuka da masana'antu daban-daban.
6. Taimakon Kai Da Kuma Yabawa
Fahimtar abubuwan da suka faru a baya da kuma yadda suke tasiri a duniya a yau zai iya haifar da tausayi da fahimta ga ƙungiyoyin mutanen da tarihinsu zai iya bambanta da na yau da kullum. Hakanan za ku fahimci wahala, farin ciki, da hargitsi sune abubuwan da suka haifar da yau wadda muke ciki a yau kuma ku yaba da duk abin da kuke iya amfana daga ƙoƙarin da mutanen da suka yi a yau.

Da kyau
ReplyDelete