Posts

Rana irin ta yau Janairu, 1924

Image
21 ga Janairu, 1924 Vladimir Lenin ya mutu  Vladimir Lenin, masanin juyin juya halin Bolshevik kuma shugaban farko na Tarayyar Soviet, ya mutu ne sakamakon zubar jini a kwakwalwa yana da shekaru 54.

RANA IRIN TA YAU A TARIHI 2/1/2023

Image
2 ga Janairu, shekarar 1492 Spain ta sake karɓo Granada A wannan rana a shekarar 1492, Granada, gidan sarautar Alhambra, fada da kuma babban birni na ƙarshe na masarautar Moorish a Spaniya , ya miƙa wuya ga Sarakunan Katolika, Ferdinand II da Isabella I , wanda ya kawo ƙarshen mamayewar da ake musu. Ƙarin haske: Moorish daga Moors sune musulman da suka mulki Spaniya, Andalus a wancan lokacin. 2 ga Janairu, shekarar 1905 Rundunar ƴan sandan Rasha ta mika wuya a tashar jiragen ruwa ta Port Arthur A lokacin yaƙin Russo-Japan ƴaki tsakanin Rasha da Japan, Port Arthur, sansanin sojojin ruwa na Rasha a ƙasar Sin, ya faɗa hannun sojojin ruwan Japan karkashin Admiral Heihachiro Togo . 2 ga Janairu, shekarar 1863  Yaƙin Stones River  Yaƙin Stones River ya zo ƙarshe a lokacin yaƙin basasar Amurka; ko da yake ba a  ayyana hakan ba, arangamar wata ce nasara ce ga sojojin ƙungiyar, waɗanda Janar William S. Rosecrans ya jagoranta. Ƙarin haske: Stones River wani rafi ne da...

Menene amfanin sanin tarihi? (2)

Image
  Yana koyar da bayyanannen darasi 1. Sanin Siyasa Tarihi zai iya taimaka mana mu zama nagartattun ƴan ƙasa masu ilimi. Ya nuna mana ko su  wanene mu a matsayinmu na gamayya, kuma sanin wannan muhimmin abu ne na tabbatar da al'ummar dimokuradiyya. Wannan ilimin yana taimaka wa mutane su taka rawar gani a fagen siyasa ta hanyar muhawara ta ilimi da kuma fayyace ainihin imanin mutane. Ta hanyar ilimin tarihi, 'yan ƙasa za su iya canza tsoffin tsarukan da aka yadda dasu a baya. 2. Tarihi Yana Koyar Da  Ɗ a'a Da  Ɗ abi'u   Ta hanyar kallon kebantaccen labarai na daidaikun mutane da yanayi, zaku iya gwada ɗabi'u da ƙimar ku. Kuna iya kwatanta shi da wasu yanayi na wahala da mutane suka fuskanta a lokutan wahala. Kallon mutanen da suka fuskanci kuma suka shawo kan wahala na iya zama da ban sha'awa. Kuna iya yin nazarin manyan mutanen tarihi waɗanda suka yi nasara ta hanyar matsalolin ɗabi'a, da kuma talakawa waɗanda ke koya mana darussa cikin ƙarfin hali, dagiya d...

Me Yasa Tarihi Yake Da Muhimmanci?

Image
Menene tarihi? Tarihi shine ilimi da nazarin abubuwan da suka gabata. Labari ne na baya. Tarihi shine labarin su wanene mu, inda muka fito, kuma yana iya bayyana inda muka dosa. Menene amfanin sanin tarihi? (1) Tarihi yana da mahimmanci don yin nazari yana da mahimmanci ga dukanmu wajen fahimtar kanmu da kuma duniyar da ke kewaye da mu. Akwai tarihin kowane fanni da batu, daga likitanci, zuwa kiɗa, zuwa fasaha. Sani da fahimtar tarihi ya zama dole. Yana ba mu damar fahimtar ƙarin sanin abubuwa da dama 1. Duniyarmu Tarihi ya ba mu cikakken hoto na yadda bangarori daban-daban na al'umma - kamar fasaha, tsarin gwamnati, da ma al'umma baki daya suka yi aiki a baya don mu fahimci yadda suka fara aiki kamar yadda yake a yanzu. 2. Al'umma Da Sauran Mutane Nazarin tarihi yana ba mu damar lura da fahimtar yadda mutane da al'ummomi suka kasance. Alal misali, za mu iya yin la’akari da yaƙe-yaƙe, ko lokacin da al’umma ke cikin kwanciyar hankali, ta wajen waiwayar abubuwan da suka f...